Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Suna Sintiri A Sokoto


'Yan sanda a Sakkwato sun kafa wuraren tare ababen hawa suna bincike, tare ad yin sintiri a kan tituna yau litinin a bayan da aka samu tashin hankali a tsakaninwasu kungiyoyin Musulmi guda biyu a birnin.

'Yan sanda a wannan tsohon birni dake arewan maso yammacin Nijeriya sun ce shaidawa Muryar Amurka cewar sun kama mkutane fiye da sittin a lokacin wannan taho-mu-gama a tsakanin kungiyoyin 'yan Shi'a da na Sunni wadda ta barke ranar jumma'a zuwa asabar.

Wasu kafofi sun ce mutane hudu sun mutu, wasu mazauna garin kuma suka ce adadin ya kai 20. Sai dai kuma jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Sakkwato, Mohammed Umar, ya shaidawa Muryar Amurka cewa ba su samu rahoton rashin rai ba.

Sakkwato dai ita ce cibiyar shugaban Musulmin Nijeriya, Sultan na Sakkwato. Shaidu sun ce wannan tashin hankali ya barke a babban Masallacin Sakkwato lokacin sallar Jumma'a, a bayan da wasu 'yan mazhabin Sunni suka hana wani shugaban 'yan Shi'a yin huduba.

Wannan shine tashin hankali na uku a tsakanin kungiyoyin biyu tun watan Maris a lokacin da aka kashe mutane akalla uku.

XS
SM
MD
LG