Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mujallar Newsweek Ta Janye Labarin Da Ta Buga Game Da Wulakanta Qur'ani


Mujallar "Newsweek" ta janye labarin da ta buga cewar wani binciken da rundunar sojojin Amurka ta gudanar ya gano shaidar cewa an wulakanta al-Qur'ani a wani gidan kurkukun soja na Amurka.

Editan mujallar, Mark Whitaker, ya ce a bisa abinda muka gano a yanzu, "mun janye wannan labari da muka buga."

Wani kakakin fadar shugaban Amurka ta White House, Scott McClellan, ya ce janye labarin "matakin farko ne mai kyau," amma kuma ya kamata mujallar ta fadi yadda aka yi ta yi kuskuren buga wannan rahoto.

Rahoton mujallar ya ce Amurkawa masu gudanar da tambayoyin da ake yi wa fursunoni a Guantanamo Bay a Cuba sun jefa al-Qur'ani cikin masai a wani yunkuri na neman hbude bakin mutanen da ake tuhuma da aikata ta'addanci. Wannan rahoto ya janyo mummunar zanga-zanga a kasashen Musulmi da dama, ciki har da Afghanistan inda aka kashe mutane akalla 17.

Minoistan yada labarai na kasar Pakistan, Sheikh Rashid Ahmed, ya fada a yau talata cewar wannan rahoto ya ci zarafin Musulmi, kuma neman gafara da janye labarin kawai ba zasu iya magance irin wannan tozartawa ba.

XS
SM
MD
LG