Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan jam'iyyar Democrat A Majalisar Dattijan Amurka Sun Ce An Katse Tattaunawa Kan Alkalai


Shugaban marasa rinjaye (Democrat) a majalisar dattijan Amurka, Harry Reid, ya tsinke tattaunawar da yake yi da 'yan jam'iyyar Republican da nufin kaucewa kai ruwa rana a game da sunayen wasu mutane da shugaba Bush ya gabatar yana neman a tabbatar musu da mukaman alkalai a kotunan tarayya.

A lokacin da yake magana da 'yan jarida, Sanata Reid, dan jam'iyyar Democrat daga Jihar Nevada, ya ce a yanzu dai za a warware batutuwan dake tattare da wadannan alkalai bakwai ne a zauren majalisar dattijan.

'Yan jam'iyyar Republican sun ce zasu nemi sauyi a tsarin tafiyar da harkokin majalisar ta yadda 'yan jam'iyyar Democrat ba zasu iya hana jefa kuri'a kan mutanen da ake son nadawa alkalai ta hanyar matakin nan da ake kira "Filibuster", watau dabarar jinkirta gudanar da wani abu a majalisa ba.

Shugaban 'yan jam'yyar Republican masu rinjaye a majalisar, Sanata Bill Frist daga Jihar Tennessee, ya ce 'yan jam'iyyarsa suna son abinda ya kira "kuri'ar amincewa ko kin amincewa cikin adalci a kan wadannan mutane."

Amma kuma 'yan jam'iyyar Democrat, wadanda ke daukar wadannan alkalai a zaman masu matsanancin ra'ayin rikau, sun ce sauya tsarin gudanar da harkokin majalisar zai zabtare ikon marasa rinjaye a cikin majalisar dattijan.

Za a iya fara tankiya sosai a tsakanin jam'iyyun biyu gobe laraba a cikin majalisa a lokacin ad Sanata Frist zai gabatar da sunayen mutane biyu da ake son nadawa alkalai.

Wannan tankiya dai ta kara tsanani a saboda imanin da aka yi cewa akwai alkali guda ko fiye da haka dake shirin yin ritaya a kotun kolin Amurka. An ce 'yan majalisar dattijai masu matsakaicin ra'ayi suna ci gaba da tattaunawa bisa fatan kulla yarjejeniya.

XS
SM
MD
LG