Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane Sun Gudu daga Gidajensu A Sakkwato


Wasu mazauna garin Sakkwato, a yankin arewa maso yammacin Nijeriya, sun arce daga gidajensu, a bayan da aka yi barazanar taba lafiyarsu.

Shugaban wannan iyali da ake kira "Group 3" Alhaji Abubakar Chika, ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Sani Abdullahi Tsafe, cewar wasu mutanen dake kiran kansu 'yan ahlul-sunna sune suka yi wannan barazanar.

A yanzu dai Alhaji Abubakar Chika tare da 'ya'ya da jikokinsa su fiye da 100 sun bar gidajensu, sun kuma nemi hukumomin 'yan sanda da su taimaka wajen kare musu rayuka da dukiyoyinsu.

Rikici ya barke ranar Jumma'a a garin an Sakkwato a tsakanin kungiyoyin Musulmi biyu wadanda ba su ga maciji da juna, ya kuma bazu zuwa ranar asabar. A yanzu dai 'yan sandan kwantar da tarzoma suna sintiri a yankunan da ake wannan tankiya.

XS
SM
MD
LG