Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zanga A Guinea-Bissau


Dubban mutane sun fito kan tituna a Gini Bissau a bayan sanarwar da hambararrern shugaban kasar, Kumba Yalla, yayi ikirarin cewar shine halaltaccen shugaban kasa da aka cire shi da karfi.

Dalibai da malumansu sun yi jerin gwano cikin ruwan sanyi suna tur da shelar da tsohon shugaban ya yi.

Amma kuma akwai wani bangare na mutanen Gini Bissau da suka yi taron nuna goyun baya gare shi duk da gargadin da aka yi.

Hafsoshin sojan Gini Bissau sun sake nanata goyon bayansu ga gwamnatin Henrique Rosa. Shekaru biyu da suka wuce aka yi juyin mulki ga gwamnatin Kumba Yalla. A watan gobe za a sake gudanar da wani zaben shugaban kasar.

XS
SM
MD
LG