Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sham Ta Musanta Cewa 'Yan Tawayen Iraqi Sun Gana Cikin Yankin Kasarta


Jami’an kasar Sham sun musanta zargin da sojojin Amurka suka yi cewar shugabannin ’yan tawayen kasar Iraqi masu yin biyayya ga Abu Musab al-Zarqawi sun gana cikin watan da ya shige a kasar Sham.

Wani jami’in ma’aikatar harkokin waje dake magana da Muryar Amurka yau laraba a Washington, ya ce tun a bara Sham take daukar dukkan matakan da zata iya domin hana ’yan tawaye shiga cikin kasar Iraqi daga yankinta. Ya ce Sham ta bukaci Amurka da ta ba ta karin hadin kai a fannonin tsaro da leken asiri, yana mai fadin cewa tsaron kasar Iraqi abin damuwa ne ga kowa da kowa a yankin.

A ranar laraba, wani jami’in sojan Amurka ya alakanta wannan taron da ake zargin cewa an yi a Sham da karuwar hare-haren ’yan tawaye a cikin Iraqi, inda aka kashe mutane fiye da 400 tun daga farkon watan nan na Mayu.

A halin da ake ciki, an kashe mutane akalla 13 yau alhamis a Iraqi, ciki har da wani sojan Amurka daya. Shi kuma ministan harkokin wajen Iran, Kamal Kharazi, ya ziyarci babban limamin ’yan mazhabin Shi’a na kasar Iraqi, Ayatollah Ali al-Sistani, a gidansa dake birnin Najaf. ba a bayar da karin bayanin tattaunawarsu ba, amma kuma dukkansu biyu sun yi kiran da a kwantar ad hankula.

XS
SM
MD
LG