Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

bangarorin Kasar Togo Suna Ganawa A Nijeriya


Sabon zababben shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe, ya saurari ka’idojin samun zaman lafiya a kasar yau alhamis daga bakin shugabannin adawa a zauren wani taron kolin da aka kira da nufin warware rikicin siyasar kasar.

A wurin wannan taron koli da ake yi a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya, madugun ’yan adawa, Gilchrist Olympio, ya ceza a iya samun zaman lafiya a kasar Togo ne kawai idan aka kawo karshen kashe-kashen da suka barke bayan zabe, aka kuma sake gudanar da zaben shugaban kasa sabo.

Mr. Gnassingbe, wanda aka bayyana a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan da ya shige, yayi kira ga ’yan adawa da su shiga cikin gwamnatin karo-karo da yake son kafawa. ’Yan adawa sun ki yarda da wannan tayi, suna masu fadin cewa an tabka magudi a zaben.

Wannan rikici da ake yi ya haddasa mummunar taho-mu-gama inda aka kashe mutane da dama, wasu fiye da dubu 20 kuma suka gudu daga kasar. Kungiyar tarayyar Kasashen Afirka da kuma Kungiyar Kasuwar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma sune suka shirya wannan taron kolin neman sasantawa.

XS
SM
MD
LG