Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Rwanda Ya Ce Kafofin Labarai Suna Bakanta Afirka


Shugaban kasar Rwanda ya zargi kafofin yada labarai na kasashen yammacin duniya da laifin bakanta Afirka cikin labarunsu tare da yin ko oho da abubuwa na ci gaba a nahiyar.

Shugaba Paul Kagame ya shaidawa zaman bude babban taro na Cibiyar Aikin Jarida ta Kasa da Kasa yau lahadi a birnin Nairobin Kenya cewar irin wadannan labarai na bakanta Afirka da ake yadawa, suna hana masu son zuba jari zuwa nahiyar.

Ya ce ga misali a kasarsa Rwanda, kafofin labarai na kasa da kasa sun bayyana kashe-kashen kare-dangi na 1994 a zaman sakamako na duhun kai da tunanin kabilanci irin na jahiliyya, a maimakon abinda ya faru na zahiri, watau kullalliyar da gwamnati ta lokacin ta shirya da gangan. Mr. Kagame ya ce irin yadda aka yi ta baza labarin shi ya sa kasashen duniya suka nuna dari-darin tsoma baki.

Shugaban na Rwanda ya roki kafofin yada labarai da su yayata kokarin da kasashen Afirka suke yi na warware matsalolin da nahiyar take fuskanta.

Cibiyar Aikin Jarida ta Kasa da Kasa ta hada hancin masu gidajen jarida da 'yan jarida da kuma jami'an gwamnati. A ranar laraba za a kammala wannan babban taro.

XS
SM
MD
LG