Wata kotu mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta rage hukumcin daurin rai da rai da aka yanke a kan wani tsohon magajin gari a kasar Rwanda, wanda aka samu da laifin kisan kare-dangi. Kotun ta mayar da hukumcin ya komo daurin shekaru 45 a kurkuku.
Masu sauraron daukaka kara a Kotun Kasa da Kasa mai bin kadin laifuffukan yaki a kasar Rwanda, sun fada a yau litinin cewa masu gabatar da kara sun kasa tabbatarwa a fili cewar Juvenal Kajeljeli yana da alhakin kisan kare-dangi.
Har ila yau, masu sauraron daukaka karar a Arusha ta kasar Tanzaniya sun gano cewar anj take hakkin Mr. Kajeljeli, a saboda ba a gaya masa irin laifuffukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba a lokacin da aka kama shi a 1998.
Kajeljeli mai shekaru hamsin da wani abu da haihuwa, shine tsohon magajin garin Mukingo a arewacin Rwanda. A shekarar 2003 an yanke masa hukumcin daurin rai da rai a saboda kisan kare-dangi, da zuga mutane domin su aikata kashe-kashe na kare-dangi.
A lokacin kashe-kashen kare-dangi da aka yi a kasar Rwanda a 1994, 'yan tsagera na kabilar Hutu sun kashe mutane kimanin dubu 800 'yan kabilar tsiraru ta Tutsi da kuma 'yan kabilar Hutu masu sassaucin ra'ayi.