Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Zai Yi tattaki Zuwa Afirka A Yau Talata


A yau talata Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, zai yi tattaki zuwa Afirka, inda zai shiga cikin masu jagorancin wani taron da aka shirya domin neman goyon baya ga ayyukan da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka take gudanarwa a yankin Darfur na yammacin Sudan.

Jiya litinin a hedkwatar MDD dake birnin New York, Babban Sakataren yayi magana da 'yan jarida a kan wannan rangadi nasa. Ya ce zai shugabanci taron masu bayar da gudumawa da za a yi ranar Alhamis a Addis Ababa, inda hedkwatar Kungiyar tarayyar Kasashen Afirka take.

Mr. Annan ya ce akwai shirye-shiryen fadada rundunar kiyaye zaman lafiya ta Kungiyar dake Darfur daga sojoji dubu biyu a yanzu, zuwa dubu takwas. Amma kuma ya ce Kungiyar ta Kasashen Afirka tana bukatar karin kudi kimanin dala miliyan 350 domin gudanar da wannan aikin.

Har ila yau kuma, babban sakataren zai yi tattaki zuwa Darfur shi da kansa, zai kuma ziyarci garin Rumbek a kudancin Sudan inda zai nazarci shirin samar da zaman lafiya da ake gudanarwa.

XS
SM
MD
LG