Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadun NATO Sun Amince Da Gudumawa Ga Ayyukan Kiyaye Zaman Lafiya A Darfur


Jakadun kasashen Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO, sun yarda da bayar da agajin da ba na kayan fada ba ga kokarin kiyaye zaman lafiyar da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka take gudanarwa a yankin Darfur na Sudan.

Babban Sakataren NATO, Jaap de Hoop Scheffer, ya ce kungiyarsu ta yarda zata samar da ababen sufuri, da horaswa da kuma ayyukan tsare-tsare ga sojojin na kasashen Afirka.

Ya ce zai gabatar da wannan tayi na agaji a wurin babban taron da za a yi jibi alhamis a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia. Har ila yau, babban sakataren na NATO ya ce kungiyarsu zata yi aiki kafada da kafada da Kungiyar tarayyar Turai a yunkurin kungiyoyin biyu na tallafawa ayyukan da ake yi a Darfur.

A jiya litinin, ministocin tsaro na Kungiyar Tarayyar Turai sun yi alkawarin bai wa sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashen Afirka karin jiragen saman sufuri da tallafi wajen tsare-tsaren ayyukansu.

XS
SM
MD
LG