Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Turai Suna Auna Yadda Faransawa Suka Ki Yarda Da Tsarin Mulkin Tarayyar Turai


Kasashen Turai suna tunani a kan makomarsu, a bayan da masu jefa kuri'a na Faransa suka yi fatali da daftarin tsarin mulkin Tarayyar Turai da gagarumin rinjaye.

Kashi 70 daga cikin 100 na masu jefa kuri'ar Faransa sun fito jiya lahadi, inda kimanin kashi 55 daga cikin 100 suka yi watsi da daftarin tsarin mulkin, wasu kimanin kashi 45 daga cikin 100 suka amince da shi.

Tilas ne kowace daya daga cikin kasashe 25 na Tarayyar Turai ta amince da wannan tsarin mulki kafin a fara yin aiki da shi. Ya zuwa yanzu, kasashe 9 sun amince da daftarin, amma kuma akasarin kasashen Tarayyar ba su jefa kuri'a kansa ba har yanzu. Kasar Netherlands ce take shirin jefa kuri'a ta gaba a kan wannan daftarin tsarin mulki.

Firayim ministan Britaniya, Tony Blair, ya ce makomar Turai da tattalin arzikinta tana fuskantar tababa. Amma kuma ya ce lokaci bai yi ba ga Britaniya ta yanke shawarar ko zata gudanar da kuri'ar-raba-gardama a kan yarjejeniyar, yana mai bayyana wannan lokaci a zaman na nazarin shawarar da Faransawa suka yanke.

A can birnin Paris, firayim ministan Faransa, Jean-Pierre Raffarin ya gana da shugaba Jacques Chirac, yayin da ake rade-radin cewar Mr. Raffarin zai yi murabus. Firayim ministan ya fito daga zauren tattaunawa da shugaban ba tare da ya ce uffan ba

XS
SM
MD
LG