Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Hare Biyu Na Kunar-Bakin-Wake Sun Kashe Mutane 25 A Iraqi


'Yan sandan Iraqi sun ce wasu hare-haren kunar-bakin-wake guda biyu da aka kai da bam a kudu da birnin Bagadaza sun kashe mutane akalla 25, wasu mutanen su akalla 100 suka ji rauni.

An kai wadannan hare-hare na yau litinin a kofar wani ginin gwamnati dake garin Hillah, kilomita 95 daga Bagadaza, babban birnin kasar. Jami'ai suka ce 'yan harin bam din sun tarwatsa kawunansu a cikin wasu tsoffin zaratan 'yan sandan Iraqi wadanda ke zanga-zangar rushe rundunarsu da aka yi.

Wadannan hare-haren bam sun taho a daidai lokacin da sojojin Iraqi masu samun goyon bayan Amurka suke binciken gidaje tare da kakkafa shingayen tarewa da binciken ababen hawa a kewayen Bagadaza, a wani yunkurin farauto 'yan tawaye.

Kungiyar al-Qa'ida a Iraqi dake karkashin jagorancin Abu Musab al-Zarqawi, dan kasar Jordan da aka fi nema bisa zargin ta'addanci, ta ce ta kaddamar da hare-hare domin mayar da martani ga farmakin na sojojin Iraqi.

A wani labarin kuma, an sako shugaban babbar jam'iyyar siyasa ta 'yan mazhabin Sunni a kasar Iraqi, a bayan da sojojin Amurka suka kama shi na wani dan lokaci. Hukumomin taron dangin da Amurka take jagoranci a Iraqi sun ce an kama Mohsen Abdul-Hamid ne bisa kuskure.

XS
SM
MD
LG