Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Ce Sham Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Samfurin Scud


Isra'ila ta ce kasar Sham, watau Syria, ta yi gwajin makamai masu linzami samfurin "Scud."

Jami'an soja na bani Isra'ila sun fada a yau Jumma'a cewar na'urorinsu na tsaron kasa ta sama sun ga an cilla wadannan makamai masu linzami na "Scud" guda uku a ranar Jumma'ar da ta shige. Jami'an suka ce daya daga cikin makaman masu linzami ya tarwatse a samaniyar Turkiyya, ya watso tarkace a kan wasu garuruwa guda biyu, amma kuma babu wanda ya ji rauni.

Babu wani kalamin da aka ji daga kasar Sham ko Turkiyya a game da wannan batu.

Jami'an bani Isra'ila sun bayyana wadannan gwaje-gwaje a zaman matakin nuna ko oho ga Amurka da Majalisar Dinkin Duniya, wadanda suka tilastawa kasar Sham ta janye sojojinta daga Lebanon a bayan kashe tsohon firayim minista Rafik Hariri a cikin watan Fabrairu.

Jami'an bani Isra'ila sun ce sun damu da cewar ana tsara wadannan makamai masu linzami samfurin "Scud" ta yadda zasu iya daukar makamai masu guba da zasu iya kaiwa cikin Isra'ila.

XS
SM
MD
LG