Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 16 A Wani Kazamin Fada A Somaliya


Jami'ai a Somaliya sun ce an kashe mutane akalla 16 a fadan da aka faro tun daga jiya litinin har zuwa yau talata a tsakanin wasu jinsunan da ba su ga-maciji da juna.

Shaidu sun ce an bai wa hammata iska ne a ciki, da kuma bayan garin Belet Weyn, mai tazarar kilomita 300 a arewa da babban birnin kasar.

Jami'ai suka ce wannan fada ya samo asali ne daga rikicin da ake yi tsakanin kungiyoyin masu gaba da juna kan amfani da wuraren kiwon dabbobi.

Somaliya ta kasance ba ta da gwamnatin tarayya tun shekarar 1991, a lokacin da kungiyoyin jinsuna suka hambarar da gwamnatin marigayi Mohammad Siad Barre. Tun daga lokacin kuwa, fadan da ake gwabzawa a tsakanin jinsuna dabam-dabam ya jefa kasar cikin fitina.

An kafa sabuwar gwamnati cikin shekarar da ta shige a kasar Kenya, amma kuma masu kishin addini da jinsuna dabam-dabam suna yin adawa da ita. Har yanzu gwamnatin ba ta koma birnin Kogadishu ba a saboda rashin tsaro a can.

XS
SM
MD
LG