Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bukin Bude taron Yaki Da Cutar Kanjamau Na Kasa A Afirka Ta Kudu


A yau talata Afirka ta Kudu take bude taron kasa na biyu kan cutar kanjamau, inda ake dokin jin jawabin da ministar kiwon lafiya zata gabatar.

Mutane fiye da dubu uku wadanda suka hada da masu bincike, da masu raujin yaki da cutar da kuma 'yan siyasa, zasu halarci wannan taron kwanaki hudu, inda zasu tattauna hanyoyi mafi nagarta na yaki da wannan mummunar cuta. An yi kiyasin cewa akwai mutane miliyan biyar masu fama da cutar kanjamau ko suke dauke da kwayar cutar dake haddasa ta a Afirka ta Kudu.

Sai dai kuma ana kyautata zaton 'yan rajin kare muradun masu fama da wannan cuta wadanda ke hankoron da a tsige ministar kiwon lafiya, Manto Tshabalala Msimang, zasu dauke hankula a zauren taron.

A farkon wannan shekara dai, ministar ta yi gargadi a game da illolin magungunan da ake yin amfani da su wajen kashe kaifin cutar kanjamau, ta kuma nemi da a fifita cin kayayyakin abinci masu kyau a maimakon shan magungunan.

Wata kungiya mai suna "Treatment Action campaign" wadda ta gurfanar da gwamnatin Afirka ta Kudu a gaban kotu domin tilasta mata ta samar da magungunan kanjamau kyauta, ta ce kalamun ministar na rashin hankali ne.

XS
SM
MD
LG