Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Ci Gaba A Harkar Fina-Finan Hausa, In Ji Aina'u Ade


An bayyana cewar harkar fina-finan Hausa ta gawurta zuwa wani matsayin da ta zamo cikakkiyar sana'a ga jaruman dake fitowa a ciki, da fardusosin dake shiryawa da dukkan masu hannu wajen shiryawa da tallar wadannan fina-finai na Hausa.

Mashahuriyar jarumar fina-finan Hausa, Aina'u Ade, ita ce ta bayyana wannan a lokacin da take tattaunawa da filin A Bari Ya Huce.

Malam Aina'u Ade, wadda ta ce ita sarauniyar ba da dariya ce, ta ce ta fara sha'awar fina-finan Hausa a lokacin da take sana'ar kitso da gyaran gashi a Kanon dabo, a inda ta fara haduwa da jaruman dake fitowa cikin fina-finan Hausa. Kafin wannan lokaci kuwa, ba ta ma taba kallon wani fim na Hausa ba.

Aina'u Ade ta fara shiga cikin fina-finan Hausa a 1997, kuma babu irin rawar da ba ta takawa, koda yake mutane sun fi saninta da fitowa a zaman mai bayar da dariya ko kuma a zaman 'yar duniya.

Za a iya sauraren hirar da aka yi da ita, kashi na farko da na biyu, idan aka matsa rubutun dake saman wannan shafi. A yi sauraro lafiya.

XS
SM
MD
LG