Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan majalisar Dokokin Bolivia Sun Nada Sabon Shugaba


An rantsar da babban jojin kasar Bolivia, Eduardo Rodriguez, a zaman shugaban rikon-kwarya, inda yayi alkawarin gudanar da zabe cikin sauri a wannan kasa da zanga-zangar makonni ta durkusar.

An rantsar da Mr. Rodriguez cikin daren alhamis a bayan da 'yan majalisar dokoki masu zaman gaggawa suka amince da takardar murabus ta shugaba Carlos Mesa.

Da farko an dakatar da wannan zama na majalisar a birnin Sucre a bayan da dakarun tsaro suka kashe wani ma'aikacin hako ma'adinai da ya doshi wannan birni domin shiga cikin zanga-zangar neman a mayar da albarkatun makamashi a hannun kamfanonin kasar.

Mr. Rodriguez shine na uku a jerin wadanda zasu iya hawa kujerar shugabancin idan shugaba ya sauka. Shugaban majalisar dattijai Hormando Vaca diez, wanda shine na daya, da kuma shugaban majalisar wakilai, Mario Cossio Cortez, na biyu a layi, duk sun ki yarda da su karbi wannan kujera.

A cikin jawabin da yayi ga 'yan majalisa da asubahin yau jumma'a, Mr. Rodriguez ya ce yayi imani abu mafi muhimmanci a yanzu shine gudanar da sabon zabe, koda yake bai ajiye takamammiyar ranar yin hakan ba.

Shugaba mai barin gado, Mr. Mesa, ya mika takardar murabus dinsa ranar litinin, yana mai fadin cewa ba zai iya ci gaba da jagorancin wannan matalauciyar kasa dake yankin tsaunukan Andes ba a saboda irin zanga-zangar da ake ci gaba da yi.

XS
SM
MD
LG