Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Da 'Yan Tawayen Darfur Sun Koma Kan Teburin Shawarwari


Gwamnatin Sudan da kungiyoyi biyu na 'yan tawaye daga yankin Darfur na yammacin kasar sun koma kan teburin shawarwarin neman zaman lafiya, a bayan katsewar watanni shida.

Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ce ta ke shiga tsakani a wannan tattaunawa da aka fara yau Jumma'a a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Wani kakaki ya ce shugaban Tarayyar Afirka mai ci, shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya, yana da kwarin guiwar cewa tattaunawar zata warware rikicin da ake fama da shi a yankin na Darfur. Shugaba Hassan Omar al-Bashir na Sudan, ya ce yana fata za a iya cimma yarjejeniya, kammalalliya, a wannan zagayen tattaunawar.

Su ma jami'an Majalisar Dinkin Duniya suna shiga cikin tattaunawar.

Zagayen baya na tattaunawar ta watse a cikin watan Disamba a bayan da 'yan tawaye suka kaurace, suna masu dora laifin barkewar sabon fada a kan gwamnati.

Yarjejeniyoyin da aka cimma a can baya sun kasa kawo karshen tashin hankali a Darfur, inda mutane fiye da dubu 180 suka mutu, wasu miliyan biyu kuma suka rasa matsuguni.

XS
SM
MD
LG