Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wulakancin Da Wata 'Yar Fim Ta Yi Mini Ya Sa Na Dage Cewar Sai Na Zamo 'Yar Fim, In Ji Safiya Musa


Jarumar fina-finan Hausa, Safiya Musa, ta ce wulakancin da wata 'yar fim din Hausa ta yi mata, shi ya karfafa mata guiwar cewa ita ma sai ta shiga cikin wannan sana'ar, musamman domin ta nunawa duniya cewa ba kowane dan fim ne yake da hali na wulakanta masu kaunarsa ko sha'awar fina-finansa ba.

A cikin hirar da ta yi da filin A Bari Ya Huce na Muryar Amurka, Malama Safiya Musa ta bayyana yadda sha'awar shiga fina-finan ta sanya ta bar makaranta, ta nemi iznin iyayenta, ta kuma samu wani shahararren Fardusa wanda ya fara sanya ta cikin fina-finan Hausa.

Ita dai Safiya haifaffiyar Kaduna ce, kuma ta bayyana tarihinta da irin fina-finan da ta fara yi, da wadanda take yi a yanzu haka.

Sannan kuma ta bayar da albishirin sabon mukaminta na Fardusa, tana mai fadin cewa a cikin 'yan makonni kadan sabon fim dinta mai suna "Gada" zai fito.

Domin jin cikakken tattaunawar da Safiya Musa ta yi da Ibrahim Alfa Ahmed, sai a matsa rubutun dake saman wannan labari. A saurari hira lafiya.

XS
SM
MD
LG