Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sake Bude Karamin Ofishin Jakadancinta A Lagos


Amurka ta sake bude karamin ofishin jakadancinta yau litinin a cibiyar kasuwanci ta Nijeriya, Lagos, kwanaki uku bayan da ta rufe shi bisa abinda jami'ai suka kira barazanar tsaro ta zahiri da aka samu.

Wasu kasashen da suka rufe kananan ofisoshin jakadancinsu dake Lagos ma a bayan da Amurka ta rufe nata sun sake budewa a yau litinin. Wadannan kananan ofisoshin jakadancin da suka hada da na Britaniya, da Jamus da Faransa suna kan titi guda da karamin ofishin jakadancin na Amurka.

Hukumomi ba su bayyana irin barazanar da aka yi wa karamin ofishin jakadancin na Amurka ba.

XS
SM
MD
LG