Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Sun Tattauna Kyautata Mulkin Jama'a A Fadin Nahiyar


Shugabannin wasu kasashen Afirka shida sun gana jiya lahadi a Nijeriya domin karbar rahoton farko daga cikin rahotannin da aka tsara da nufin kawo karshen zarmiya da cin hanci tare da kyautata mulkin jama'a a nahiyar.

Shugaba Olusegun Obasanjo ya karbi bakuncin takwarorinsa na Afirka ta Kudu, da Aljeriya da Saliyo da Ghana da kuma Rwanda a Abuja, babban birnin kasar.

An shirya wannan rahoto na farko ne a kan yadda al'amura suke gudana a Ghana da Rwanda.

Kasashen Afirka 16 sun rattaba hannu kan shirin kyale 'yan'uwansu su auna kamun ludayinsu a fannin kawo karshen zarmiya da cin hanci, da kawar da yin rub da ciki kan kudaden baitulmali da kuma gudanar da ayyukan raya kasa masu nagarta.

Ana gudanar da wannan shiri na auna kamun ludayin kasashen ne a karkashin Sabon Kawancen Raya Kasashen Afirka, ko NEPAD, na Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka.

Nan gaba a cikin wannan shekara za a gabatar da rahotanni a kan kasashen Mauritaniya da Kenya.

XS
SM
MD
LG