Shugaban kasar Kenya ya bayar da umurnin da a binciki masu harhada barasa a boye a duk fadin kasar, a bayan da mutane 48 suka mutu a sanadin shan wata giyar da aka hada ta da ruwan magani na Methanol domin kara mata karfi.
Shugaba Mwai Kibaki ya bayyana wadanda suka hada wannan barasar da cewa makwadaita abin duniya ne, yana mai fadin cewa binciken da ya umurci a gudanar zai yi kokarin samo hanyar kawar da irin wannan matsala a nan gaba.
'Yan sanda sun ce sun kama mutane uku wadanda ake zargin su na da hannu a lamarin.
Mutane 48 sun mutu a bayan da suka sha wannan barasa mai kama da gogoro cikin 'yan kwanakin da suka shige a gundumar Machakos mai tazarar kilomita 60 a kudu da Nairobi, babban birnin Kenya.
Akwai wasu mutanen da dama suna jinya a asibiti, ciki har da mutane akalla 8 wadanda aka ce sun makance baki daya.
Irin wannan barasa mai arha da ake hadawa a boye cikin gidaje, wadda 'yan Kenya ke kira "Chang'aa" ta zamo gama gari a kasar. A shekarar 2000, mutane fiye da 100 sun mutu a bayan da suka sha irin wannan barasa hadin gida a Nairobi.