Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Doke Morocco - Zata Fuskanci Argentina A Wasan Karshe


Wasan Nijeriya da Morocco
'Yan kwallon Flying Eagles na Nijeriya sun rankadawa takwarorinsu na kasar Morocco duka da ci uku da babu a wasan kusa da karshe na gasar cin kofin kwallon kafar matasa na duniya da ake yi a kasar Netherlands.

A yanzu, ’yan Nijeriya ne zasu buga wasan karshe na neman daukar wannan kofi tare da ’yan kasar Argentina, wadanda tun farko suka doke Brazil da ci 2 da daya.

Wannan shine karo na biyu da Nijeriya take zuwa wasan karshe na cin wannn kofi. A shekarar 1989, Nijeriya ta buga wasan karshe da kasar Portugal, amma ta kasa daukar wannan kofi a lokacin.

Kwach din ’yan Nijeriya kuma tsohon shahararren dan wasa Samson Siasia, yana fata a wannan karon, hakar Nijeriya zata cimma ruwa.

Taye Taiwo, gwarzo a wasan Nijeriya da Ukraine, shi ne ya fara jefawa Nijeriya kwallo a cikin minti na 34 da fara wasa. Bayan da aka komo daga hutun rabin lokaci kuma, Olubayo Adefemi da Chinedu Ogbuke suka kara wa Nijeriya kwallaye biyu. Haka aka tashi daga wannan wasa da ci uku da babu.

Za a buga wasan karshe ranar asabar. A wasan neman wadda zata yi ta uku kuma, Brazil zata gwabza da Morocco.

XS
SM
MD
LG