Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaben Shugaba Olusegun Obasanjo


Olusegun Obasanjo
Kotun koli ta Nijeriya ta tabbatar da nasarar da shugaba Olusegun Obasanjo ya samu a zaben 2003, ta yi watsi da ikirarin da babban abokin takararsa yayi cewar an tabka magudi.

Babban mai shari'a na Nijeriya, Muhammadu Uwais, ya ce an gudanar da zaben kamar yadda Dokar Zabe ta Nijeriya ta tanada, ya kuma watsar da karar da tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja kuma shugaban hamayya Muhammadu Buhari ya shigar.

Hukumcin na yau Jumma'a, wanda dukkan alkalan kotun suka amince da shi, ya tabbgatar da yhukumcin da wata kotun karama ta yanke tun da fari cewar magudin da aka gano an yi a lokacin zaben na 2003, bai kai yadda zai iya canja sakamakon wannan zabe ba.

An gabatar da wannan hukumci yau a Abuja babban birnin kasar, inda 'yan sanda cikin damara suka dauki tsauraran matakan tsaro a ciki da kuma wajen wannan kotun.

An fara zaben shugaba Obasanjo, wanda shi kansa tsohon shugaban gwamnatin soja ne, a shekarar 1999 a zaben da ya kawo karshen mulkin soja a kasar.

XS
SM
MD
LG