Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Kasashen Afirka Ta Bullo Da Shirin Neman Kujeru A Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya


Ministocin harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, KTKA, sun bullo da wani sabon shirin da zai bai wa nahiyar kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD.

Ministocin sun cimma wannan ne jiya asabar a lokacin ganawar da suka yi a birnin Sirte na kasar Libya. A bayan wadannan kujeru biyu na dindin kuma, Afirka tana son a ba ta kujeru guda uku wadanda ba na dindindin ba ne a cikin Kwamitin Sulhun.

Wannan shirin da ministocin an KTKA suka amince da shi, ya zarce wani shirin da kasashen Brazil, Jamus, Indiya da Japan suka gabatar wanda shi kuma zai bai wa kasashen Afirka kujeru guda biyu kacal wadanda ba na dindindin ba ne a cikin Kwamitin Sulhu.

A yanzu haka dai Kwamitin Sulhun na MDD mai wakilai 15 yana da kujerun dindindin guda biyar ne wadanda duk wadda take kansu tana iya hana zartas da duk abinda ba ta so ta hanyar hawa kujerar-na-ki. Masu kujerun su ne Amurka, Britaniya, Faransa, Rasha da China.

Ministocin harkokin wajen na Afirka sun gana ne kafin taron kolin KTKA da za a yi litinin da talata a birnin na Sirte.

XS
SM
MD
LG