Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tun Ina Yaro Nake Taka Rawa A Harkar Wasan Kwaikwayon Hausa - Inji Jarumi Shehu Hassan Kano


Jarumin fina-finan Hausa, Alhaji Shehu Hassan Kano, ya bayyana cewar tun yana aji hudu a makarantar firamare ya fara shiga cikin harkar wasan kwaikwayo irin na dabe, abinda ya zamo harsashin sha'awarsa ta shiga harkar fina-finan Hausa, inda ya zamo daya daga cikin gwarzayen da suka fi burge masu kallo.

A cikin hira ta musamman da yayi da filin "A Bari Ya Huce..." na Sashen Hausa, Alhaji Shehu Kano, wanda ya fara shiga harkar fina-finan Hausa tun farkon fara yinsu, ya ce marubuta littattafan soyayya na Hausa, kamar su Ado Ahmed Gidan Dabino, Dan'azumi Baba, marigayi Aminu Hassan, sune suka fara gabatar da ra'ayin yin fina-finai a saboda ganin yadda jama'a ke sha'awar littatafansu.

Alhaji Shehu Hassan Kano, yayi bayanin fim din da ya fi burge shi, da irin rawa mafi muhimmanci da ya taba takawa, da abubuwan da suka fi wuya cikin harkar fina-finan Hausa da makamantansu.

Domin jin wannan cikakkiyar hira da suka yi da Ibrahim Alfa Ahmed, sai a taba rubutun dake saman wannan labari.

XS
SM
MD
LG