Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Ruwa Yayi Hatsari dab Da Gabar Kasar Kamaru


Gidan rediyon Kamaru ya bayar da rahoton cewa mutane har 30 ne suka mutu ko suka bace a bayan da wani karamin jirgin ruwa yayi hatsari a mashigin ruwan Guinea a dab da gabar Kamaru.

Gidan rediyon ya bayar da rahoto yau talata cewar wasu mutanen su 30 sun kubuta da rayukansu, kuma ana jinyarsu a wani asibiti kusa da wurin.

Rahoton ya ce wannan jirgin ruwa ya taso ne daga Nijeriya a kan hanyar zuwa Gabon sai ya kife jiya litinin da maraice a kusa da kauyen masunta na Campo dake kudu maso yammacin Kamaru.

Rahoton ya ce wannan karamin jirgin ruwa yana dauke da 'yan Nijeriya, da Mali da kuma Benin a lokacin da ya kife ya nutse.

Ba a dai san abinda ya janyo wannan hatsari ba. 'Yan Afirka ta yamma da dama dake neman ayyukan yi sun saba bi ta mashigin ruwan na Guinea a kan hanyarsu ta zuwa kasashen Gabon da Kamaru domin neman aiki.

XS
SM
MD
LG