Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Hare-Haren Bas Da Jiragen Karkashin Kasa A London Ya Zarce Hamsin


Hukumomi a London sun ce yawan mutanen da suka mutu a hare-haren bam da aka kai ranar alhamis kan wata motar safa ta fasinja da kuma jiragen karkashin kasa, ya zarce hamsin, sun kuma tabbatar da cewa mutane fiye da 700 sun ji rauni.

Kwamishinan 'yan sanda na London, Ian Blair, ya ce bam din da ya tashi a cikin motar safa mai hawa biyu ya kashe mutane 13. Ya ce an bar wasu gawarwakin a cikin taragan jiragen karkashin kasa da suka tarwatse yayin da injiniyoyi ke kokarin tabbatar da cewa ramukan ba su rushe a kan ma'aikata ba, su kuma masu bincike suna bin dukkan tarkacen dake karkashin gano ko za su gano shaidar wanda ya aikata wannan abu.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce bama-baman da aka yi amfani da su kanana ne (masu kimanin nauyin kilo hurhudu), kuma babu wata alamar ko harin na kunar-bakin-wake ne, koda yake ya ce ba za a iya tantance cewar ba hakan ba ne.

Tun da fari, kwamishinan ya ce bama-baman sun yi kama da aikin kungiyar ta'addanci ta al-Qa'ida, amma kuma yayi hasashen za a jima ana gudanar da aikin bincike mai sarkakiya kan lamarin. Wata kungiyar da ba san da zamanta ba a can baya, wadda ke kiran kanta "Kungiyar Sirri ta Jihadin al-Qa'ida a Turai" ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare a wani sakon da aka buga kan wani dandalin harshen larabci a duniyar gizo (Internet).

A halin da ake ciki, rayuwa ta fara komawa kamar ta da a London. Motocin safa na fasinja suna aiki, yayin da wasu jiragen na karkashin kasa su ma suka fara aiki.

XS
SM
MD
LG