Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Olusegun Obasanjo Ya Ce an Samu Gagarumar Nasara A Taron Kolin Kasashe Masu Arzikin Masana'antu Na Duniya


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya ce an samu gagarumar nasarar taron kolin kungiyar kasashe masu arzikin masana'antu ta G8 da aka gudanar a Gleneagles a kasar Scotland.

A karshen taron kolin an kwanaki biyu da shugabannin kasashe masu arzikin masana'antu suka yi, Mr. Obasanjo ya godewa firayim minista Tony Blair na Britaniya da sauran shugabannin kungiyar ta G8 a saboda shirin bayar da agaji ga Afirka da suka bullo da shi, wanda ya hada da dala miliyan dubu hamsin, da yarjejeniya kan cinikayya da kuma yafe basussuka.

Shugaba Obasanjo ya ce shugabannin Afirka sun yi farin cikin ganin cewa mummunan ta'addancin da aka aikata kan Britaniya bai kawar da hankulan shugabannin kasashen G8 daga abinda suka kudurta yi ba, yana mai mika jajensa ga Britaniya da kuma mutanen da suka rasa 'yan'uwansu ko suka jikkata a hare-haren.

Mr. Obasanjo ya jaddada kudurin shugabannin Afirka na yaki da ta'addanci.

XS
SM
MD
LG