Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tony Blair Zai Yi Jawabi Ga Majalisar Dokoki Dangane Da Hare-Haren Ta'addanci Na Makon Jiya A London


Firayim minista Tony Blair na Britaniya zai yi jawabi ga majalisar dokoki dangane da hare-haren bam an ta'addanci da aka kai a London cikin makon da ya shige, yayin da a wani gefen ake ta yin kiraye-kirayen kaddamar da bincike kan yadda matakan tsaro suka kasa hana wannan lamari.

A lokacin da ta ke magana da gidan rediyon Britaniya a yau litinin, sakatariyar harkokin cikin gida, Hazel Blears, ta yi watsi da bukatar binciken matakan tsaro, tana mai fadin cewa yin hakan zai iya gurgunta hukumomin 'yan sanda da na tsaron kasar.

Shugabannin hamayya na Britaniya sun ce irin wannan bincike zai taimaka wajen gyara matakan tsaro masu sako-sako da 'yan harin suka yi amfani da su wajen aikata wannan ta'asa wadda ta kashe mutane akalla 49, wasu guda 700 suka ji rauni.

Kwararrun masu binciken kimiyya sun ce za a shafe makonni kafin a gano sunayen dukkan mutanen da aka tsinci gawarwakinsu ko wasu gabobinsu. Ya zuwa yanzu dai sun gano sunan mutum guda ne kawai, wata mace 'yar kasar ta Ingila mai shekaru 53 da haihuwa.

A halin da ake ciki, magajin garin birnin London, Ken Livingstone, ya zamo mutum na farko da ya sanya hannu a cikin littafin jaje ga wadanda suka mutu ko suka jikkata, inda ya rubuta cewar "birnin London zai murmure."

XS
SM
MD
LG