Wakilai daga yankin kudancin Nijeriya mai arzikin man fetur sun kauracewa zama na karshe na babban taron sake fasalin siyasar kasar da aka yi wata guda ana gudanarwa, a saboda rashin jituwa kan yadda za a raba dukiyar mai a kasar.
Wakilan da suka fito daga yankin Niger Delta sun fice daga zauren taron a yau litinin a bayan da aka ki biya musu bukatar da suka nema ta a ba su akalla kashi 25 daga cikin 100 na dukkan kudin da za a samu daga man fetur a kasar.
Wakilai daga sauran sassan kasar sun yarda ne kan cewa za a bai wa jihohin wannan yanki kashi 17 na dukkan kudin mai, watau karin kashi 4 daga cikin 100 daga kashi 13 da ake ba su a yanzu.
Ana fama da rashin kwanciyar hankalin a yankin na kudancin Nijeriya, har ma kungiyoyin sojojin sa kai a yankin sun yi barazanar yin tawaye idan har ba a kara yawan arzikin man da ake ba su ba.
Wannan taro na sake fasalin siyasar Nijeriya ya kunshi 'yan siyasa, da 'yan rajin kare muradu dabam-dabam da kuma shugabannin addini daga fadin kasar, kuma an shirya shi ne da nufin kawo shawarwari a kan yin gyara ga tsarin mulki.