Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Laura Bush Ta Fara Ziyara A Kasashen Afirka


Laura Bush
Uwargidan shugaban Amurka, Laura Bush, ta fara rangadin kasashe uku a nahiyar Afirka. Zangonta na farko shi ne birnin Cape Town a Afirka ta Kudu, inda ta gana da iyaye mata wadanda ke dauke da kwayar halittar cuta ta HIV mai janyo kanjamau.

Mrs. Bush ta yi tattaki zuwa unguwar share-ka-zauna mai suna Khayelitsha a bayangarin Cape Town domin ganawa da wadannan mata matasa da kuma wasu matan masu fama da cutar kanjamau kuma masu juna. Wannan cibiya dake samun tallafin kudin gudanarwa daga Amurka, tana bayar da tallafi ga iyaye mata wadanda ke dauke da cutar kanjamau, ciki har da wayar da kai tare da horaswa kan yadda zasu guji harbin 'ya'yan dake cikinsu da wannan kwayar cuta.

Daga baya, Mrs. Bush zata gana da 'yan Afirka ta Kudu dake kokarin kawo karshen yadda wasu mazaje ke cin zarafin matansu.

An tsara wannan rangadin na uwargida Laura Bush ne da nufin kara bayyanawa duniya sabbin shirye-shiryen shugaba Bush na yaki da cutar kanjamau da wasu cututtukan a nahiyar Afirka.

Gobe laraba Mrs. Bush zata zarce zuwa tanzaniya, daga nan kuma ta wuce zuwa kasar Rwanda.

XS
SM
MD
LG