Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan tawaye Sun Ci Gaba Da kai Munanan Hare-Haren Kunar-Bakin-Wake A Iraqi


An ci gaba da kai hare-haren kunar-bakin-wake yau lahadi a Iraqi, yayin da mutanen wani gari a kudu da Bagadaza suke kokarin gano gawarwakin mutanen da suka kone kurmus jiya asabar a wani mummunan harin bam a Musayyib.

Dan harin bam na jiya asabar ya tayar da bam dinsa daidai kusa da wata motar tanka dauke da fetur, yayi kaca-kaca da tsakiyar garin na Musayyib, ya kashe mutane akalla 70, wasu fiye da 80 suka ji rauni.

Yau lahadi a Bagadaza, an kashe ’yan Iraqi su akalla 8 a wasu hare-haren bam a kan motocin ’yan sanda da na sojojin Iraqi. A wani harin dabam kuma, an bayar da rahoton kashe sojan Amurka daya, wasu biyu suka ji rauni a sanadin bam da aka dana a gefen hanya a Kirkuk.

A halin da ake ciki, firayim ministan Iraqi, Ibrahim al-Jaafari, yana ganawa yau a birnin Teheran da shugaban Iran mai barin gado, Mohammed Khatami. Ana sa ran shugabannin biyu ’yan mazhabin Shi’a zasu sanya hannu a kan muhimman yarjejeniyoyin makamashi, ciki har da guda wadda zata kyale a shimfida bututun da zai dauko man da aka tace daga yankin tsakiyar Asiya ya bi ta cikin Iran zuwa Iraqi.

A wani labarin kuma, kotun musamman ta Iraqi ta gabatar da tuhumar farko a kan Saddam Hussein dangane da laifuffukan da aka aikata a cikin shekaru 24 da yayi yana mulkin kasar. Babban alkali mai bincike ya ce an tuhumi hambararren shugaban dangane da mutuwar mutane da dama a kauyen Dujail a 1982. Hukumomi sun yi zargin cewa an kashe mutanen kauyen ne a zaman ramuwar gayya bayan da aka yi yunkurin kashe Saddam Hussein.

Alkalin ya shaidawa ’yan jarida cewar nan da ’yan kwanaki za a bayyana ranar shari’ar.

XS
SM
MD
LG