Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Ta Doshi Senegal


Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Condoleeza Rice, zata yi tattaki zuwa Senegal talatar nan, zangonta na farko a rangadin kasashe shida wanda zai kai ta har Sudan da Isra'ila da yankunan Falasdinawa.

A Senegal, Ms. Rice zata halarci wani taron da za a yi a Dakar, babban birnin kasar, kan huldar cinikayya a tsakanin Amurka da kasashen Afirka a karkashin shirin Amurka na bunkasa cinikayya da Afirka wanda ake kira AGOA a takaice.

Daga nan zata doshi Sudan a inda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce zata yi kokarin karfafa aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya mai dimbin tarihi ta wannan shekara wadda ta kawo karshen yakin basasar shekaru 21 a tsakanin gwamnati da tsoffin 'yan tawayen kudancin kasar.

Har ila yau Ms. Rice zata yi rangadin yankin yammacin kasar na Darfur, inda wani tawayen dabam ya janyo mutuwar dubban mutane, wasu fiye da miliyan biyu kuma aka ce sun rasa matsuguni.

A yankin Gabas ta Tsakiya, sakatariyar harkokin wajen zata gana da manyan shugabannin bani Isra'ila da na Falasdinawa kan shirin Isra'ila na janyewa daga zirin Gaza da kuma wasu unguwannin kama-wuri-zauna guda hudu na yahudawa dake yankin Yammacin kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG