Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Shari'ar Wasu Mutane 16 A Kasar Kwango Brazzaville Kan Kashe-Kashen Kare Dangi


An fara shari’ar wasu mutane 16 a kasar Kwango Brazzaville a saboda rawar da ake zargin sun taka wajen kisan ’yan gudun hijira fiye da 300 a shekarar 1999. Amma kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil Adama guda uku, wadanda suka fara tono wannan magana a Faransa, suna kauracewa shari’ar.

Wakiliyar Muryar Amurka a Paris, Lisa Bryant, ta aiko da rahoton cewa har yanzu ba a ga gawarwakin mutane 353 da aka yi zargin an kashe ba, jim kadan a bayan da suka koma gidajensu daga gudun hijirar da suka yi a kasar Kwango ta Kinshasa makwabciyarsu. Amma kuma kungiyoyin kare hakkin bil Adama na Faransa sun ce babu shakka an aikata wannan kisan kare dangi a wani gari mai suna Beach a kasar Kwango Brazzaville.

Shekaru shida bayan wannan, wata kotu a birnin Brazzaville ta fara shari’ar wadannan mutane 16, cikinsu har da wasu manyan jami’an gwamnatin Kwango saboda hannun da ake zargin suna da shi a wannan kisa. Jamhuriyar Kwango ta ce wannan shari’a, wadda za a nunawa duniya ta telebijin, za a gudanar da ita tsakani da Allah.

Amma kuma wani lauya dan kasar Faransa, Patrick Baudoin yayi tur da wannan shari’a a zaman ta bogi kawai. Mr. Baudoin shine tsohon shugaban Tarayyar Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama ta kasa da kasa mai hedkwata a birnin Paris. An gayyaci tarayyarsu domin ta zamo daya daga cikin masu shigar da kara a wannan shari’a ta Brazzaville. Amma kuma ya ce babu wani sukuni na yin shari’ar gaskiya, kuma idan sun shiga, tamkar sun halalta wannan shari’a ce kawai.

Tarayyar Kungiyoyin Kare hakkin Bil Adama ta kasa da kasa tana daya daga cikin kungiyoyin da suka shigar da kara a Faransa, ba wai a Kwango Brazzaville ba, game da wannan kisan kare dangi na garin Beach a 2001. Sun yi zargin cewa manyan jami’an gwamnatin Kwango suna da hannu a bacewa da kuma kisan mutane 353, dukkansu wadanda ake zaton ’yan adawa ne a lokacin yakin basasar Kwango na dan gajeren lokaci.

Lauya Baudoin ya ce wannan kara da suka shigar ta samu karin karfi daga shaidar wasu mutane guda 6 da aka ce wai sun kubuta da rayukansu daga wannan kisan kare dangi, wadanda a yanzu kuma suke da matsayin ’yan gudun hijira a Faransa.

Mr. Baudoin ya ce tana yiwuwa shugaba Dennis Sassou Nguesso na Kwango yana da masaniya game da wannan kisan kare dangi, amma kuma bai yi wani abu na hana abkuwar hakan ba. A lokacin, Mr. Sassou Nguesso ya shaidawa abokan adawar siyasarsa da suka gudu cewar zasu iya komawa cikin kasar babu wanda zai taba lafiyarsu. Hukumomin Kwango sun musanta aikata wani laifi a wannan lamarin.

XS
SM
MD
LG