Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiyar Agaji Ta Majalisar Dinkin Duniya Ta Nuna Takaicin Rashin Tallafawa Jamhuriyar Nijar


Wata hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, tana zargin kasashen duniya da kasa taka rawar gani wajen tallafawa yunkurin samar da cimaka a Jamhuriyar Nijar. Yunwa na yiwa sama da kashi biyu bisa uku na al’ummar kasar barazana, amma hukumar agajin jinkai ta majalisar tace 'yan kudade kalilan kawai ta samu daga cikin abinda ta bukata watanni da dama da suka shige domin ciyar da mutane a Nijar.

Wakilin Muryar Amurka a Abidjan, Joe Bavier, ya ce Jamhuriyar Nijar ta shafe shekara guda tana fama da karancin abinci, sakamakon kamfan ruwa da kuma farin dango da suka yi barna a gonaki. Wannan ya haddasa yunwa kamar yadda Hukumar Kula da Ayyukan agajin Jinkai ta MDD ta yi gargadi tun farko cewa hakan na iya faruwa.

Kimanin mutane miliyan biyu da dubu dari biyu ne ke fama da mummunan karancin abinci a kasar. Ousmane Toudou, wani dan jarida na Nijar, ya ziyaraci wadansu daga cikin sassan da abin yafi muni, ya kuma ce "Matsalar tana da girma ainun ga mutanen Nijar, abin yayi muni ainun. Kuma wadanda abin ya fi shafa sune kananan yara."

Malam Toudou ya kara da cewa, "Akwai kananan yara da shekarunsu basu wuce hudu ba da suka zama kamar tsofaffi domin yunwa. Yunwa ta nakasa su, har ma zaka ga cikinsu sun yi ritsitsi, idanunsu kuma sun yi kwarmi."

Duk da kirayen kirayen da Hukumar Kula da Ayyukan Jinkai ta MD ta yi tun wuri, jami’anta sun bayyana cewa, ba a sami wata gudummuwar kirki ba. Na’ibar kakakin hukumar dake Afrika ta Yamma, Ute Kollies, tace duka duka, kudin da suka samu bai kai dala miliyan shidda daga cikin miliyan talatin da suke bukata ba. Ta kara da cewa, "Idan ka duba za ka ga cewar abinda ake bukata domin ceton ran yaro guda daya da yunwa ta nakkasa, dalar Amurka tamanin ne kawai, kudin da bai taka kara ya karya ba, kuma ina jin cewa kasashen duniya da duk wani mai hali, ya kamata ya taimaka. Jean Zeigler wata mai kula da shirin samar da abinci ta ziyarci Nijar kwannan nan ta ishe yaran da kafin wannan lokacin, nauyinsu ya kai tsakanin kilo shidda zuwa bakwai yanzu duka duka nauyinsu bai wuce kilo uku ba. A wata cibiyar ta ga yara goma sha hudu sun mutu daga cikin yara sittin da daya da yunwa ta kwantar."

Ms Kollies ta bayyana cewa, duk da yake lamarin yana da muni a halin yanzu, idan ba a sami tallafi daga kasashen duniya cikin gaggawa ba, abin zai kara baci. Ta ce su na bukatar yin wani abu cikin gaggawa. Kuma za a yi amfani da dukan kudin da aka samu nan take ko a sayi hatsin da aka yi amfani da shi ko kuwa raba kayan masarufi ga mabukata.

Shugaban ofishin kula da Ayyukan Jinkai na MDD, Jan Egeland, ya bayyana cewa kafin mako shidda da suka shige cibiyar bata sami gudummuwar ko anini ba. Wadansu kwararrun aikin agaji suna cewa ba a sami kyakkywan goyon bayan tallafawa jamhuriyar Nijar ba sakamakon bala’in guguwar tsunami da aka yi watan disamban bara. Suka ce yawancin kudin da za a bada agaji an karkatashi zuwa tallafawa wadanda bala’in tsunami ya shafa.

XS
SM
MD
LG