Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Misra Tana Farautar Wadanda Suka Kitsa Hare-Hare


Misra ta fara farautar mutanen da suka kitsa hare-haren bam da suka kashe mutane akalla 88, tare da raunata wasu kimanin 200 jiya asabar a wani wurin shakatawa dake bakin gabar tekun maliya.

An kama mutane da dama, kuma ana ci gaba da kai sumame yau lahadi a ciki da kuma kewayen garin Sharm El sheikh inda aka kai hare-haren.

Shugaba Hosni Mubarak na Misra ya yi rangadin wurin, 'yan sa’o’i kadan a bayan da bama bamai guda uku suka ragargaza wani otel mai kayan alatu da kuma wani wurin saye-saye. Ya ce wadannan hare-haren zasu karfafa kudurin kasar Misra na zakulowa tare da murkushe ta’addanci tun daga tushe.

Jami’an Misra sun ce wasu ’yan kunar-bakin-wake sun tayar da bama-bamai da aka dana cikin mota, yayin da a daidai lokacin wani bam da aka dana da wani agogo ya tashi.

Akwai ’yan kasashen waje su akalla 8 a cikin wadanda aka kashe.

Ma’aikatan gaggawa sun ce ba su tsammanin zasu samu wani da rai a yanzu, an kuma tura manyan motocin kwashe shara domin su kwashe burbushin gine-ginen da suka rushe.

A halin da ake ciki, ’yan sanda sun ce wani mutumin kasar ta Misra ya ji rauni mai tsanani yau lahadi a birnin al-Qahira a lokacin da bam da yake dauke da shi ya sullube ya fadi kasa ya kuma tashi.

XS
SM
MD
LG