Babban baturen ’yan sanda na birnin London ya nemi gafarar iyalan wani mutumi dan kasar Brazil wanda ’yan sanda suka kashe a lokacin da suka ce sun zaci dan harin kunar-bakin-wake ne, amma kuma iyalan mutumin sun ce tuba kawai ba ta biya ba.
Babban jami’in rundunar ’yan sandan London, Ian Blair, ya bayyana takaicinsa ga iyalan mutumin a wata hirar da aka watsa yau lahadi, amma kuma ya ce za a ci gaba da yin aiki da umurnin da aka bai wa ’yan sanda na harbewa tare da niyyar kashewa, a bayan hare-haren kunar-bakin-wake na ’yan kwanakin nan.
An kashe Jean Charles de Menezes dan kasar Brazil mai shekaru 27 da haihuwa ranar Jumma'a a lokacin da aka ce ya gudu wa ’yan sanda masu fararen kaya a wata tashar karkashin kasa. Wani dan’uwansa yayi watsi da furucin babban jami’in ’yan sandan yana mai bayyana kisan a zaman rashin iya aiki na ’yan sanda.
Gwamnatin Brazil ta nemi cikakken bayani, kuma ministan harkokin wajenta yana ganawa da jami’an Britaniya a London kan wannan harbi.
A halin da ake ciki, ’yan sanda sun tayar da nakiyar da suka dasa jikin wata jakar da ba su yarda da ita ba a wata unguwar dake arewa maso yammacin London. Jami’ai suka ce watakila wannan jaka tana da alaka da hare-haren bam na kwanakin nan.