Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Jigila Na Amurka Ya Koma Zirga-Zirga A Sararin Samaniya


Yau aka harba jirgin jigila a sararin samaniya na Amurka mai suna Discovery, a karon farko da Amurka take tura dan sama jannati zuwa samaniya tun bayan hatsarin jirgin jigila mai suna Columbia a shekara ta dubu biyu da uku.

A cikin wata sanarwa, shugaba Bush ya godewa Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, a saboda dawo da shirin jigilar jiragen na sararin samaniya. Yace tashin jirgin jigila na Discovery a yau yana da muhimmanci ga ci gaba da kasancewar Amurka jagorar sauran duniya wajen zirga-zirga da kuma binciken sararin samaniya.

Hukumar Binciken Sararin Samaniya, NASA, ta ce ba ta fuskanci matsalar gejin mai wadda a farkon watan nan ta sanya mata ala tilas ta dakatar da shirin harba jirgin jigilar ba.

Sama da kamarori dari ne suka dauki hotunan harba jirgin ta kusurwoyi dabam-dabam a yau domin ganin ko akwai wata alamar burbushi irin wanda ya lalata fiffiken jirgin jigilar Columbia shekaru biyu da rabi da suka shige.

Wannan lalacewar fiffike ita ce ta sanya jirgin jigila na Columbia ya kama da wuta ya kashe dukkan ’yan sama jannati 7 dake cikinsa a lokain da yake komowa doron kasa daga shawagi a samaniya.

Jirgin jigila na Discovery da ya tashi yau dauke da 'yan sama jannati bakwai zai yi kwana goma sha biyu a sararin samaniya, zai kuma kai kayayyaki zuwa tashar binciken kimiyya a sararin samaniya ta kasa da kasa.

XS
SM
MD
LG