Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liberiya Da Makwabtanta Biyu Sun Bukaci Nijeriya Da Ta Mika Hambararren Shugaba Charles Taylor


Liberiya da wasu makwabtanta biyu sun bukaci Nijeriya da ta mika hambararren shugaban Liberiya, Charles Taylor, domin a gurfanar da shi a gaban Kotun Bin Kadin Laifuffukan Yaki ta Majalisar Dinkin Duniya mai zama a kasar Saliyo.

Shugabannin Liberiya da Saliyo da kuma Guinea sun ce Mr. Taylor ya karya yarjejeniyar da ta kyale shi ya koma zaman hijira a Nijeriya shekaru biyu da suka shige. Sun yi zargin cewa yana ci gaba da yin katsalanda a harkokin dukkan kasashen uku, ya kuma yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2003 wadda ta kawo karshen yakin basasar Liberiya.

A jiya jumma'a shugabannin kasashen uku suka bayar da sanarwar haka a bayan taron kolin da suka yi a Freetown, babban birnin Saliyo. Wadanda suka rattaba hannu kan wannan sanarwa sun hada da shugaba Ahmed Tejan Kabbah na Saliyo; da shugaban rikon kwarya na Liberiya, Gyude Bryant, da kuma Firayim Ministan Guinea, Cellou Diallo, wanda ya sanya hannu a madadin shugabansa, Janar Lansana Conte.

Ana tuhumar Mr. Taylor da aikata laifuffukan yaki dabam-dabam a saboda rawar da ya taka a yakin basasar da aka jima ana yi a kasar Saliyo. Daga cikin wadannan laifuffukan da ake zargin ya aikata har da daukar yara aikin soja da ba su kwayoyi masu gusar da hankali, da karfafawa sojojinsa guiwar yin fyade da nakkasa jama'a domin tsoratar da su.

XS
SM
MD
LG