Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dukkan 'Yan Majalisar Wakilan Tarayya Ta Nijeriya Su 360 Sun Yarda Zasu Bayar Da Gudumawa Ga Masu Fama Da Yunwa A Nijar


A Nijeriya, 'yan majalisar wakilai ta tarayya sun yarda kowa zai ciro kudi daga aljihunsa ya bayar gudumawa ga makwabciyarsu Jamhuriyar Nijar mai fama da bala'in yunwa, a yayin da karin agaji, musamman daga Faransa yake isa Maradi, daya daga cikin wuraren da aka fi fama da wannan bala'i.

Dukkan 'yan majalisar wakilan tarayyar Nijeriya su 360 sun yarda zasu bayar da gudumawar da ta zarce dalar Amurka dubu hamsin daga aljihunsu ga masu fama da yunwa a Nijar.

A yayin ad wannan ke faruwa ne kuma Faransa da wasu kasashen suke daukar karin matakai na taimakawa Nijar a yayin da wannan bala'i ke kara yin tsanani a wannan kasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka.

A jiya asabar shugaba Jacques Chirac na Faransa ya ce kasarsa zata ninka yawan agajin abincin da take bai wa Nijar har sau uku a bana zuwa agajin dala miliyan biyar da dubu dari uku. Mr. Chirac ya fada cikin wata sanarwar da ya aikewa da shugaba Mamadou Tandja na Jamhuriyar Nijar cewa Faransa zata kuma ninka yawan agajin da take bai wa Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya.

A jiya asabar, wani jirgin saman Faransa dauke da ton goma sha takwas na abinci ya sauka a Maradi.

Ita ma kasar Canada ta yi alkawarin bada Hukumar Abincin kudi dala dubu dari takwas ta kuma roki sauran kasashe masu magana da harshen Faransanci da su dauki matakan magance matsalar yunwa a Nijar.

XS
SM
MD
LG