Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Gwamnati Da 'Yan Tawayen Ivory Coast Sun Koma Tattaunawa


Shugabannin sojojin gwamnati da na 'yan tawayen kasar Ivory Coast sun koma kan teburin shawarwari, a wani yunkuri na tsara shirin kwance damarar yaki da aka jima ana jinkirtawa, wanda kuma a yau lahadi ya kamata a ce an fara gudanar da shi.

Dukkan sassan sun ce har yanzu suna kokarin tantacewa tare da amincewa da adadin cibiyoyin da 'yan tawaye da dakaru masu biyayya ga gwamnati zasu je su domin mika makamansu.

Tsarin lokacin da dukkan sassan suka amince da shi, ya tanadi cewa ya zuwa yanzu ya kamata a ce mayakan 'yan tawaye da masu biyayya ga gwamnati sun fara komawa wuraren da aka kebe domin ajiye su na wucin gadi.

Tsarin lokacin yayi kira ga mayakan da su mika makamansu ga sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a cikin watan Satumba.

Zaman tankiya ta karu a tsakanin gwamnatin Ivory Coast da 'yan tawayen kasar a bayan wasu hare-hare da aka kasa gane kansu a kan dakarun tsaro cikin makon da ya shige.

XS
SM
MD
LG