Hafsoshin sojan kasar Mauritaniya sun ce sun hambarar da shugaba Mouawiya Ould Sid Ahmed Taya.
A yau laraba wata kungiya dake kiran kanta Majalisar Adalci da Dimokuradiyya ta Soja ta bayar da sanarwar juyin mulkin a kafofin labarai na gwamnatin kasar. Har ila yau majalisar ta ce sojoji za su tafiyar da mulkin kasar na tsawon shekaru 2.
Tun da fari a yau laraba, sojoji a Nouakchott, babban birnin Mauritaniya, sun kwace tasoshin rediyo da telebijin na kasar, tare da wasu muhimman gine-gine a yayin da shugaban yake Sa’udiyya wajen jana’izar sarki Fahd.
An ji karar harbe-harbe na dan wani lokaci kadan yau laraba a kusa da fadar shugaban kasar, yayin da aka ga sojoji cikin damara sosai a kewayen birnin.
A halin da ake ciki, shugaba Ould Sid Ahmed taya ya sauka a Jamhuriyar Nijar makwabciyarsa.
Shugaban na Mauritaniya ya sha tsallake rijiya da baya a yunkure-yunkuren juyin mulkin da aka yi masa a cikin shekaru 20 da yayi yana mulkin kasar. A watan Yunin shekarar 2003, ’yan tawaye sun zo dab da hambarar da shi daga kan karagar mulki, a lokacin da aka yi kwanaki da dama ana gwabzawa a kan titunan babban birnin kasar.
A cikin ’yan kwanakin nan, shugaba Maaouya yana daukar matakan murkushe masu yin adawa da mulkinsa, cikinsu har da sojoji da kungiyoyin kishin addinin Islama.