Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Majalisar Sojoji mai Mulkin Mauritaniya Ta Sako masu Kishin Islama Su 20


Sabuwar majalisar soja mai mulkin kasar mauritaniya ta sako masu kishin addinin Islama su kimanin 20, wadanda hambararren shugaba Maaouiya Ould Sid'Ahmed Taya ya daure a kurkuku.

Gungun mutane masu nuna farin ciki sun tarbi mutanen da aka sako, kwanaki hudu a bayan da hafsoshin soja suka kifar da gwamnatin shugaba Ould Taya wanda ya jima yana mulkin kasar.

Masu sukar lamiri sun ce shugaba Ouldmasu yin adawa da shi.

A halin da ake ciki, madugun masu juyin mulkin, Ely Ould Mohammed Vall, ya nada sabon firayim ministan da zai maye gurbin Sghair Ould M'Bareck, wanda yayi murabus yau lahadi.

Kanar Vall ya nada jakadan Mauritaniya a kasar Faransa, Sidi Mohammed Ould Boubacar, a zaman sabon firayim minista.

Sabuwar gwamnatin ta soja ta yi alkawarin gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a cikin shekaru biyu, ta kuma ce babu wani jami'inta da zai tsaya takarar zabe. Amma duk da haka, Amurka da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, sun yi kiran da a maido da gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.

XS
SM
MD
LG