Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci Suna Duba Mayakan Ruwa Na Rasha Su Bakwai Da Aka Ceto Daga Karkashin Teku


Dukkan mayakan ruwa 7 da suka makale cikin wani jirgin karkashin ruwa na Rasha, har na tsawon kwanaki uku a can karkashin teku, sun iso bakin gaba lami lafiya a bayan da aka gudanar da aikin ceto su daga can karkashin tekun.

Jami’an Rasha suka ce da alamun mutanen suna da cikin koshin lafiya. A yanzu haka dai likitoci suna duba su a tashar jiragen ruwan Petropavlovsk-Kamchatsky dake kuryar gabashin Rasha, inda aka kai su a cikin jirgin ruwa bayan da suka taso saman teku.

Wani jirgin ceto a karkashin ruwa na Britaniya, wanda ake sarrafa shi da na’urar Rimot, shine ya nutsa ya yanke wayoyi da igiyoyin da suka sarkafe jirgin karkashin ruwan na Rasha a can karkashin teku. Jirgin karkashin ruwan ya taso sama da kansa bayan da aka tsinke wayoyin.

Mutane bakwai dake cikinsa sun fito da kansu, kuma da alamun koshin lafiya im ban da gajiyar da aka gani a fuskokinsu.

Hukumomin Rasha sun godewa Britaniya da Amurka da kuma Japan a saboda amsa kiran da suka yi na taimakawa wajen ceto mutanen. Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana godiya maras iyaka musamman ga wadanda suka yi aiki kai tsaye wajen ceto mutanen.

Jami’an Rasha sun ce a ranar alhamis, dan karamin jirgin karkashin ruwan ya sarkafe cikin wayoyin eriya na soja dake karkashin teku da kuma wata makekiyar koma ta masunta da wasu suka jefar cikin teku. Wayoyi da igiyoyin sun rike wannan jirgin a can doron teku, mita 200 daga doron kasa, kuma ba tare da iskar shaka na lokaci mai tsawo ba.

Hotunan bidiyo na wannan aikin ceto sun nuna jirgin a sarkafe da igiyoyi ta ko ina. Kafofin labarai na Rasha sun ce shugaba Vladimir Putin ya bayar da umurnin a gudanar da bincike kan abinda ya haddasa wannan hatsari.

XS
SM
MD
LG