Sabon tashin hankali ya jijjiga kasar Iraqi a yau laraba, a yayin da wa’adin ranar litinin na rubuta sabon daftarin tsarin mulki yake kara kusantowa.
’Yan sanda sun ce an kashe mutane shida, cikinsu har da ’yan sanda su akalla biyu, a lokacin tashin wani bam da aka boye cikin mota a wata unguwa mai suna Ghazaliya a yammacin Bagadaza. Mutane su akalla bakwai sun ji rauni a wannan harin.
Ita kuma rundunar sojojin Amurka ta bayar da sanarwar cewa a yau laraba ne ta kawo karshen farmakin hadin guiwa na farauto ’yan tawaye wanda ta kaddamar tare da sojojin Iraqi a yankin yammacin kasar.
Rundunar ta ce an tsare mutane 36 wadanda ake jin cewa ’yan tawaye ne domin yi musu tambayoyi. Har ila yau an gano bama-baman da ake boyewa cikin mota guda 9 da wasu bama-baman guda 28 a lokacin wannan farmaki.
Amurka da kuma gwamnatin Iraqi suna fatar cewa sabon tsarin mulkin dimokuradiyya da za a zana zai taimaka wajen kawo karshen wanan tawaye da ’yan mazhabin Sunni suke jagoranci, amma kuma har yanzu bangarorin kasar ta Iraqi dake kokarin zana wannan daftari, sun kasa cimma daidaitawa kan muhimman batutuwa da dama.