Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Madugun 'Yan Kudancin Sudan A Zaman Babban Mataimakin Shugaban Kasa


An rantsar da madugun 'yan kudancin Sudan, Salva Kiir Mayardit, a zaman babban mataimakin shugaban kasa, inda ya maye gurbin John Garang wanda ya mutu a wani hatsarin jirgin sama helkwafta a watan da ya shige.

A yau tsohon kwamandan sojojin 'yan tawayen yayi rantsuwar yin biyayya ga jamhuriyar Sudan a wurin wani bukin da aka gudanar a Khartoum, babban birnin kasar.

Ya lashi takobin zai bi akidojin Mr. Garang tare da kokarin ganin an samu zaman lafiya da hadin kai a Sudan.

Shugaba Hassan Omar al-Bashir na Sudan, da karamin mataimakin shugaban kasa Ali Osman Taha sun hadu da Mr. Mayardit suna tafawa. Daga nan mutanen uku sun rike hannun juna suka daga sama domin nuna cikakken hadin kansu.

Wannan karamin buki ya sha bambam da wanda aka yi wata guda da ya shige a lokacin da aka rantsar da Mr. Garang. Mr. Garang ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati a watan Janairu domin kawo karshen yakin basasar shekaru 21.

XS
SM
MD
LG