Accessibility links

Tsohon Madugun 'Yan Tawayen Hutu Na Burundi Ya Ajiye Mukaminsa


Tsohon madugun 'yan tawayen kabilar Hutu na kasar Burundi, Pierre Nkurunziza, ya ayyana ajiye mukaminsa na madugun 'yan tawaye a yayin da yake shirin zamowa shugaban kasar.

A jiya jumma'a Mr. Nkurunziza tare da wasu tsoffin mayaka 40 suka mika makamansu a wurin wani bukin da aka shirya na kwance damarar yaki a Muramuya.

Tsohon maduhgun 'yan tawayen, wanda yake jagorancin kungiyar nan mai suna "Dakarun Kare Dimokuradiyya" ko FDD a takaice, shi kadai yake takara a zaben shugaban kasar Burundi da za a yi ranar 19 ga watan nan na Agusta.

FDD ta doke dukkan abokan adawar siyasarta a zabubbuka na yankuna da na kasa baki daya da aka yi cikin watannin Yuni da Yuli, ta samu gagarumin rinjaye a majalisun dokoki na tarayya, matakin da ya sa babu wanda zai iya zama shugaban kasa sai shi Mr. Nkurunziza.

An kashe mutanen da yawansu ya kai zambar 300 a yakin basasar shekaru 12 a kasar Burundi, wanda a yanzu wata kungiya kwaya daya tak ta 'yan kabilar Hutu ce mai suna national Liberation Forces take gudanar da shi. Wannan yaki na Burundi ya barke a bayan da sojojin kasar wadanda 'yan kabilar Tutsi 'yan tsiraru suka kanainaye, suka kashe shugaban kasar dan kabilar Hutu wanda aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.

XS
SM
MD
LG