Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban 'Yan Sandan Isra'ila Sun Toshe Hanyoyi A Fadin Kudancin Kasar


Dubban 'yan sandan kasar bani Isra'ila sun tare manyan hanyoyin mota a fadin kudancin kasar lahadin nan domin hana yahudawa 'yan tsagera sukunin gurgunta shirin Isra'ila na kwashe yahudawa daga Zirin Gaza.

A cikin yankunan Falasdinawa kansu, an fara girka 'yan sandan Falasdinu a kewayen unguwannin share-ka-zauna na 'yan Isra'ila domin hana Falasdinjawa kai hari a kan 'yan kaka-gidar da aka shirya zasu fara barin Gaza daga litinin din nan.

Hukumomin Isra'ila sun ce har yanzu akwai dubban 'yan kaka-gida a cikin Gaza, tare da wasu 'yan tsageran yahudawa su dubu hudu masu yin adawa da janyewar, wadanda suka lashi takobin tayar da kayar baya.

A gobe litinin Isra’ila zata rarraba takardun umurnin kwashe dukkan mutanen dake zaune a unguwannin kwace ka zauna 21 a Gaza da kuma guda hudu a yankin yammacin kogin Jordan karkashin shirin firayim minista Ariel Sharon na janyewa daga yankunan da yake ganin ba su da wani amfani ga tsaron kasar.

’Yan kaka gidan da aka ba su wannan notis suna da kwanaki biyu, watau zuwa ranar laraba, na su tattara nasu ya nasu su fice kafin a tura jami’an da zasu je su fitar da wadanmda suka ki karfi da yaji.

XS
SM
MD
LG